IQNA

Karatun Al-Qur'ani na Dan wasan Manchester United

19:29 - March 17, 2023
Lambar Labari: 3488825
Tehran (IQNA) Bidiyon karatun kur’ani mai tsarki da Amir Ibragimov dan wasan kungiyar Manchester United Academy ya yi, ya samu karbuwa sosai daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sawa Al-Akhbariya cewa, hoton dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Amir Ibragimov yana karatun kur’ani mai tsarki ya samu karbuwa sosai daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ingila ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter tare da nuna hoton dan wasan Manchester United Amir Ibragimov da ke karatun kur'ani mai tsarki, yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta sun kwatanta muryarsa da muryar Sheikh Saleh bin Muhammad Al-Hidan.

Idan dai ba a manta ba, Amir, dan shekara 15 musulmi, an haife shi a shekara ta 2007, memba ne a makarantar Manchester United kuma yana da tarihin kasancewa a fagen kai hare-hare a wannan kungiyar kuma ya yi nasara a kan Liverpool.

 

 

4128342

 

captcha