IQNA

Jawabin Jagora na Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyyah a hubbaren Imam Ridha

15:29 - March 19, 2023
Lambar Labari: 3488833
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musuluncin zai gabatar da jawabi a ranar Talata 1 ga Afrilu, 1402, a daidai lokacin da ake shiga sabuwar shekara, a hubbaren Iamm Ridha (AS) da kuma taron masu ziyara .

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin Musulunci a ranar Talata 1-04-1402 a daidai lokacin da ake shiga sabuwar shekarar shamsiyyah, jagoran juyin juya hali na Iran zai gabatar da jawabi a hubbaren .

Wannan shiri tare da halartar dimbin ma'abota ibada da maziyarta na haramin zai fara ne da karfe 15:00 da karfe 16:00 zai jagoran juyin juya halin Musulunci zai gabatar da jawabinsa, wanda za a watsa bayanin wannan shirin kai tsaye daga kafafen yada labarai na shafin KHAMENEI.IR da gidajen rediyo da talabijin.

Ya kamata a sani cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci bai yi tafiya zuwa Mashhad ba a cikin kwanakin Nowruz tsawon shekaru uku da suka gabata saboda shawarwarin kiwon lafiya don hana yaduwar cutar Corona, kuma a ranar farko ta Afrilu 2019 zuwa 1401. ya yi magana da al'ummar Iran kai tsaye da kuma ta talabijin.

 

4128948

 

captcha