IQNA

Sakon bidiyo na kungiyar Hizbullah ta Lebanon zuwa Tel Aviv

14:36 - July 17, 2023
Lambar Labari: 3489490
Beirut (IQNA) A ci gaba da zagayowar ranar samun nasara a yakin kwanaki 33 kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da wani sako na bidiyo mai tsawon mintuna 6 mai taken "La Ghalib Lakum" inda ta yi kwatankwacin wani harin turjiya a wani wuri na gwamnatin sahyoniyawan tare da lalata shi gaba daya.

Shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Alam ya bayar da rahoton cewa, a jajibirin zagayowar ranar samun nasarar kungiyar Hizbullah a kasar Labanon a yakin kwanaki 33 a shekara ta 2006 (Yakin Tammuz) kungiyar Islamic Resistance Movement ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta saki wani bidiyo da ke nuni da yadda mayakan kungiyar suka tarwatsa wani shinge na sojojin yahudawan Isra’ila.

 

 

 

 

captcha