IQNA

Kyautar Kur'ani Ga Tauraron Dan Wasa Na Kasar Saudiyya

15:00 - August 17, 2023
Lambar Labari: 3489656
Riyadh (IQNA) Tauraron dan wasan kasar Faransa na kungiyar Al-Ittihad na kasar Saudiyya ya karbi kwafin kur’ani mai tsarki a matsayin kyauta daga wani dan jaridar kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na News Masr cewa, dan jaridar kasar Saudiyya Ebrahim Al-Farian ya mika kyautar kur’ani mai tsarki a cikin harshen Faransanci ga Karim Benzema, tauraron dan kwallon Faransa na kungiyar Al-Ittihad Jeddah.

Elfarian ya saka wani bidiyo a shafinsa a dandalin X (tsohon Twitter) yana nuna shi yana ba da kyauta ga Benzema yayin da yake tafiya tare da rakiyar.

Dan jaridar kasar Saudiyya ya rubuta a kan wannan bidiyo cewa: Na ba shi kwafin kur’ani mai tsarki da aka fassara zuwa Faransanci.

Kwanaki biyu da suka wuce, bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ittihad da Al-Raed, Elfarian ya baiwa Fabinho agogon Rolex.

Karim Benzema yana daya daga cikin shahararrun musulmi a fagen wasanni. A shekarun baya, gaisuwar bukukuwan Musulunci da hotunan ziyarar da Benzema ya kai aikin Hajji ya samu karbuwa daga masu amfani da shafukan sada zumunta na musulmi.

A ranar 16 ga watan Agusta bayan kammala halartar wannan kungiya a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Sarki Salman ya ziyarci birnin Makka da gudanar da aikin Umrah.

A wancan lokacin Benzema ya fitar da wani faifan bidiyo a dandalin sada zumunta na X a lokacin da yake gudanar da aikin Hajji Umrah, inda yake dawafin Ka'aba a cikin tufafin Ihrami.

A cikin ‘yan watannin nan dai ci gaba da tozarta kur’ani mai tsarki da aka yi a kasashen turai, ya yi zafi a zukatan al’ummar musulmi a duk fadin duniya, kuma a kafafen yada labarai an yi ta samun labarai daban-daban na martanin musulmi dangane da wannan cin mutuncin.

 

 

 

4163093

Abubuwan Da Ya Shafa: kur’ani dan wasa dandali kyauta riyadh umrah
captcha