IQNA

Sanarwar hadin gwiwa ta zaman tare tsakanin Kirista da Musulmi a Tunisiya

21:18 - August 17, 2023
Lambar Labari: 3489659
Tunis (IQNA) Daruruwan mabiya darikar katolika na kasar Tunusiya tare da dimbin musulmin kasar sun jaddada zaman tare da juna a wani tattaki da suka gudanar..

Babban labarin jaridar Daily Sabah na cewa, bayan da rikici ya barke a kasar Tunusiya kan batun bakin haure, daruruwan mabiya darikar Katolika wadanda yawancinsu bakaken fata ‘yan Afirka ne, tare da dimbin musulmin kasar Tunusiya sun gudanar da wani tattaki domin nuna goyon bayansu ga zaman tare, inda suka bayar.

Daruruwan bakin haure ‘yan Afirka kudu da hamadar Sahara da ke zaune a Tunisia sun rasa ayyukansu da gidajensu, an samu rahotannin kai hare-hare, sannan dubbai sun tsere zuwa kasashensu bayan da shugaban kasar Tunisiya Qais Said ya yi jawabi kan bakin haure a watan Fabrairu.

A farkon watan Yuli, an kori wasu daruruwan mutane daga birnin Sfax kuma jami'an tsaron Tunisiya sun kwashe su zuwa yankin hamadar da ke kan iyaka da Libya, inda a kalla 27 daga cikin wadannan bakin haure suka mutu, wasu 73 kuma suka bace.

Dangane da haka, kungiyar kare hakkin bil'adama mai zaman kanta ta Human Rights Watch ta bayyana irin mumunan cin zarafi da jami'an tsaron Tunusiya suke yi kan bakin haure 'yan Afirka bakar fata, ta kuma bukaci kungiyar Tarayyar Turai da ta dakatar da goyon bayan da take ba wa kasar nan wajen ba da kayayyakin kudi a yaki da bakin haure.

A cikin rahoton na wannan kungiya, duka, kame ba bisa ka'ida ba, satar kudi, kamawa, korar jama'a, ayyuka masu hadari a cikin teku, da tilasta musu fitar da su na daga cikin munanan cin zarafi da wadannan dakaru suke yi kan bakin haure na Afirka, wanda ya kamata ya tilasta wa Tarayyar Turai daina ba da tallafi ga kasar nan wajen yaki da bakin haure.

 

 

 

 

4163045

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi kirista zaman tare tattaki hadin gwiwa
captcha