IQNA

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da bude ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya a Bahrain

16:21 - September 06, 2023
Lambar Labari: 3489771
Beirut (IQNA) A yayin da take yin Allah wadai da bude ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya a birnin Manama, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa, an aiwatar da wannan mummunan aiki da ya sabawa muradun al'ummar Bahrain da kuma imaninsu.
Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da bude ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya a Bahrain

A rahoton al-Mayadeen, kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa: Matakin da gwamnatin Bahrain ta dauka na bude ofishin jakadancin makiya haramtacciyar kasar Isra'ila ya faru ne a mafi munin matakin da wannan gwamnatin ta wucin gadi take ciki.

Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa: Muna yin Allah wadai da wannan ha'inci da kuma kara jaddada cewa al'ummar Bahrain da al'ummar kasarmu suna adawa da duk wata alama ta daidaitawa da alaka da makiya.

Hizbullah ta jaddada cewa: Sahayoniyawan ba za su samu mafaka a kasarmu ba.

Kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa: Wannan cin amana kamar wuka ne ga al'ummar Palastinu, wadanda suke rayuwa cikin mafi girman almara da jaruntaka a wannan zamani na fuskantar ta'addancin sahyoniyawan.

Bayanin na Hizbullah ya ci gaba da cewa: Wannan mugunyar aiki yana nuna gaskiyar wannan tsari da ke gaggawar daidaitawa da makiya, kuma hakan ya sabawa manufofin al'ummar Bahrain da akidarsu. Bayan shekaru da dama na danniya da ta'addanci a kan al'ummar Bahrain, gwamnatin ta bude ofishin jakadanci ga gwamnatin makiya.

 

 

 

4167260

 

captcha