IQNA

Korar mutumin da ya keta alfarmar kur'ani mai tsarki daga kasar Sweden

15:59 - October 27, 2023
Lambar Labari: 3490049
Hukumomin kasar Sweden sun sanar da cewa ba za su sabunta takardar izinin zama dan gudun hijira dan kasar Iraki kirista da ya wulakanta Kur'ani a wannan kasa ba, kuma za a kore shi daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, hukumar kula da shige da fice ta kasar Sweden ta sanar da cewa, ba a sabunta takardar izinin zama na Selvan Momika, wani dan kasar Iraki kirista da ya kona kur’ani mai tsarki a kasar sau da dama, kuma bayan karewar wa’adinsa na zama, za a fitar da shi daga kasar.

Tashar talabijin ta Sweden TV4 ta sanar a kan haka cewa an dakatar da Momika daga komawa Sweden na tsawon shekaru 5 bayan korarasa.

A wannan lokacin ne, a cewar gidan rediyon Sveriges, wannan dan gudun hijira na Iraki yana shirin yin zanga-zangar adawa da wannan matakin.

Tashar talabijin ta SVT ta Sweden ta kuma kara da cewa an karbi wannan dan kasar Iraki a matsayin bakon haure a kasar Sweden a watan Afrilun 2021 kuma ya samu takardar izinin zama na tsawon shekaru uku.

A baya SVT ta ruwaito cewa an kira Momika zuwa hukumar shige da fice kuma a watan Agusta an yi ganawar sa’o’i da yawa da shi.

Idan dai ba a manta ba Selvan Momika dan kasar Iraki kirista ya kona kur’ani mai tsarki sau da dama a cikin ‘yan watannin da suka gabata, wanda ya fuskanci kakkausar suka daga musulmin duniya.

Gwamnatin Iraqi dai ta bukaci hukumomin kasar Sweden da su tasa keyar wannan mutumin tare da mika shi ga Iraqi domin a yi masa shari'a a wannan kasa.

 

4178054

 

captcha