IQNA

Gwamnatin Falastinu Ta Bukaci Tarayyar Turai Da Ta Amince Da Kafa Kasar Falastinu

22:41 - March 11, 2020
Lambar Labari: 3484611
Gwamnatin kwaryakwaryan cin gishin kai ta Falastinawa, ta bukaci kungiyar tarayyar turai da ta amince da kafuwar kasar Falastinu mai cin gishin kanta.

Jaridar Quds al-arabi ta bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen Falastinu Riyad Almaliki ya aike da wata wasika zuwa ga babban jami’i mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar, inda  acikin wasikar ya bukaci tarayyar da ta amince da kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta a kan iyakokinta na shekara ta 1967.

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a kan batun rikicin Falastinawa da Isra’ila a ranar 23 ga wannan wata na Maris, da nufin duba hanyoyin mayar da dukkanin bangarorin biyu kan teburin tattaunawar sulhu da zaman lafiya.

Riyad Almaliki ya bayyana cewa, gwamnatin Falastinu tana jinjina wa matakan da kungiyar tarayyar turai ta dauka a lokuta da dama, na nuna goyon baya ga falastinawa, da kuma nuna goyon baya ga batun kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta.

3884835

 

captcha